logo

HAUSA

Wakilin Sin Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Martaba ‘Yancin Kai, Tsaro Da Cikakkun Yankunan DRC

2022-10-06 16:55:43 CMG Hausa

Da yake jawabi a yayin taron tattauna rahoton babban kwamishinan kare hakkin dan Adam da kwararru kan Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) a yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam na MDD karo na 51, da aka gudanar a ranar 5 ga watan Oktoba, wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya, da su martaba ‘yancin kai da tsaro da cikakkun yankunan kasar Jamhuriyar demokiradiyar Congo(DRC).

Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa, ci gaban da aka samu game da halin da ake ciki a kasar, ya shafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakiya da kudancin Afirka da ma nahiyar Afirka baki daya. Kasar Sin tana fatan bangaroin da abin ya shafa a DRC, za su ci gaba da matsa kaimi wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba da daidaita bambance-bambance ta hanyar tuntuba da tattaunawa.

Har kullum kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Afirka da su rika warware matsalolin Afirka ta hanyar da ta dace da Afirka, tana kuma goyon bayan DRC wajen raya tattalin arzikinta da inganta zaman rayuwar jama’a da tinkarar annoba daban-daban, kana ta riga ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya don su shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a DRC.

Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai tare da kasashen duniya don bayar da gudummawar da za ta kai ga tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da ci gaba  mai dorewa. (Ibrahim)