logo

HAUSA

Najeriya na sa ido game da bullar Ebola a Uganda

2022-10-05 15:47:34 CMG Hausa

 

Mahukuntan lafiya a tarayyar Najeriya, sun ce suna lura matuka game da bullar cutar Ebola a kasar Uganda tun daga watan Satumban da ya gabata.

Da yake tsokaci game da hakan cikin wata sanarwa, shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ko NCDC Ifedayo Adetifa, ya bayyana cewa, ma’aikatan dake lura da sashen yaki da cutar Ebola na cibiyar sun gudanar da binciken tantance yanayi, game da shirin kasar na tunkarar wannan annoba.

Adetifa ya kara da cewa, akwai yiwuwar bazuwar cutar cikin Najeriya, saboda shige da ficen fasinjoji ta jiragen sama tsakanin kasashen Najeriya da Uganda, musamman ma ta filin jirgin saman Nairobi na kasar Kenya, cibiyar yankin gabashin Afirka, da sauran kasashe masu makwafta da Uganda.

To sai dai kuma, jami’in ya ci gaba da cewa, Najeriya na da ikon tunkarar wannan kalubale, idan har aka samu bullar cutar a kasar. Ya ce an tsara bibbiyar yanayin lafiyar fasinjojin da suke shiga Najeriya ta Uganda har tsaron kwanaki 21, domin tabbatar da ba sa dauke da kwayoyin cutar Ebola mai haifar da zubar jini. (Saminu Alhassan)