An sake tabo shawarwarin tabbatar da tsaron duniya da raya duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar yayin babban taron MDD
2022-10-05 09:20:28 CMG Hausa
A makon da ya gabata ne, aka kammala muhawarar babban taron MDD na bana, inda mambobi wakilan kasashe 190 suka yi jawabai bisa taken "Lokaci mai cike da sarkakiya: hanyoyin kawo sauyi ga kalubalen da suka dabaibaye juna.”
A jawabin da ya gabatar yayin taron muhawara na babban taron MDD karo na 77, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya sake yin bayani kan shawarwarin tabbatar da tsaron duniya da raya duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, inda ya zayyana manufofi shida, wadanda suke tabbatar da wanzar da zaman lafiya a maimakon rikici, da raya kasa a maimakon talauci, da bude kofa ga ketare a maimakon rufe kofa, da gudanar da hadin gwiwa a maimakon nuna kiyayya, da hada kai a maimakon kawo baraka, da tabbatar da adalci a maimakon nuna fin karfi, manufofin dake nuna matsayin kasar Sin game da muhimman batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa.
Shugaban babban taron MDD karo na 77 Korosi Csaba, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, sun yaba wa muhimmiyar rawar da kasar Sin ta dade tana takawa, wajen goyon bayan manufar tafiyar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, da samun dauwamammen ci gaba da sauransu.
Ana haka ne kuma, wasu rukunin kasashe suka jaddada rashin amincewarsu, a yayin zaman kwamitin kare hakkin dan-Adam na MDD karo na 51 da yanzu haka ke gudana a birnin Vienna, kan yadda wasu kasashe ke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Suna masu cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, da Hong Kong da Tibet, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kuma bai kamata a rika siyasantar da batun hakkin dan Adam da nuna ma'aunai biyu ko tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam ba.
Wata sanarwar hadin gwiwa da kasar Pakistan ta gabatar a madadin kasashe 68, ta jaddada cewa, mutunta ikon mulki, da 'yancin kai da cikakkun yankuna da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na kasashe masu cin gashin kansu, na daga cikin muhimman ka'idojin da suka shafi dangantakar kasa da kasa.
Ya kamata dukkan bangarori su martaba manufofi da ka'idojin yarjejeniyar MDD, da kiyaye ka'idojin kasa da kasa, da rashin nuna son kai, da nuna gaskiya da adalci, da mutunta 'yancin jama'ar kowace kasa na zabar hanyar samun ci gaba daidai da yanayin kasashensu, da rashin nuna bambanci, da ba muhimmanci ga 'yancin tattalin arziki, da zamantakewa da al'adu da kuma musamman 'yancin ci gaba. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)