logo

HAUSA

Bai kamata a maida Iraki fagen takarar siyasa tsakanin bangarori daban daban ba

2022-10-05 16:35:26 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Dai Bing ya bayyana a jiya cewa, yankin da kasar Iraki ke ciki yana da muhimmanci, ganin yadda ke kunshe da kabilu da mabiya addinai da dama, don haka ya kamata a mai da kasar a matsayin mai dinkin yankin da take ciki, a maimakon fagen takarar siyasa tsakanin bangarori daban daban.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a yayin da kwamitin sulhun MDD yake bincike kan batun kasar Iraki, inda ya ce kasar Sin ta yaba wa Iraki bisa kokarin ta na sada zumunta, da sa kaimi ga hadin gwiwa a yankin da take ciki, kana ta nuna goyon bayan matakin kasashen Iraki da Kuwait, a aikin da suke yi na kokarin gano wasu ‘yan kasar Kuwait da suka bace, da maido da dukiyoyin kasar Kuwait.

Ya ce Sin tana tsayawa tsayin daka, kan manufar kiyaye ikon mulkin kai, da cikakkun yankunan kasa ciki har da na kasar Iraki, tana kuma son ganin yadda ake kiyaye tsaro ta hanyar hadin gwiwa.

Dai Bing ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Iraki tana cikin lokaci mai muhimmanci a fannin siyasa, wanda cikin sa ake fuskantar manyan ayyuka, kamar kafa sabuwar gwamnati. Don haka kasar Sin ke fatan bangarori daban daban na kasar Iraki, za su kara hadin gwiwa, da daidaita matsalolinsu, da cimma daidaito kan harkokin siyasa, ta hanyar yin shawarwari bisa kundin tsarin mulki da dokokin kasar, ta yadda za a kai ga aza tubalin siyasa, a kokarin samun zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa da wadata a kasar. Ya ce ya kamata sassan kasa da kasa su girmama ikon mallakar yankunan kasar Iraki, su nuna goyon baya ga jama’ar kasar wajen zaben hanyoyin bunkasa kasarsu masu dacewa da yanayin ta. (Zainab)