logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Dauki Sabbin ‘Yan Sama Jannati Da Za Su Gudanar Da Binciken Sararin Samaniya A Nan Gaba

2022-10-03 15:55:05 CMG Hausa

Hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin (CMSA), ta sanar a jiya Lahadi cewa, kasar za ta dauki sabbin ‘yan sama jannati 12 zuwa 14, wadanda za su gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya a nan gaba.

Daga cikin ‘yan sama jannatin da ke cikin shirin ko-ta-kwana, kana rukuni na hudu na ‘yan sama jannatin kasar, bakwai zuwa takwas daga cikinsu za su kasance matuka kumbunan sama jannati, biyar zuwa shida daga cikinsu za su kasance injiniyoyin kumbunan sama jannati da kwararru masu kula da gwaje-gwaje, ciki har da guda biyu a matsayin kwararru masu kula da gwaje-gwaje, a cewar CMSA.

A cewar hukumar, za a dauki matuka kumbunan sama jannati ne daga cikin matuka dake aikin soja.

Za a zabo injiniyoyin kumbunan sama jannatin ne daga cikin wadanda ke gudanar da ayyukan binciken kimiyya da aikin injiniyan sararin samaniya da sauran bangarori da abin ya shafa, yayin da kwararru masu kula da gwaje-gwaje, za su fito ne daga masu bincike dake dora muhimmanci kan kimiyyar sararin samaniya da dai sauransu.

A matsayinta na mai shirya daukar ma’aikatan, a karon farko hukumar CMSA, za ta zabo kwararru masu kula da gwaje-gwaje daga yankunan musamman na Hong Kong da Macao na kasar Sin.

A cewar CMSA, ana sa ran kammala daukar sabbin ‘yan sama jannati ne a cikin shekara daya da rabi. (Ibrahim)