logo

HAUSA

Guterres ya yi kira da a samar da zaman lafiya da mutunta juna yayin ranar rashin tashin hankali ta duniya

2022-10-03 16:27:58 CMG Hausa

 

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga a samar da zaman lafiya da mutunta juna, yayin da ake bikin ranar rashin tashin hankali ta duniya.

A sakon da ya gabatar ya bayyana cewa, ranar rashin tashe-tashen hankalu ta duniya, ba wai ranar haihuwar Mahatma Gandhi kawai ba ne, amma rana ce da ake murnar yayata dabi’unsa wanda aka amince da su a shekarun nan da suka gabata, wato zaman lafiya da mutunta juna, da muhimmancin mutantawa da kowa ke nunawa.

Ya kara da cewa, wannan duniya, ba ta dace da wadannan dabi’u ba, yana mai cewa, ana ganin haka ta irin rikice-rikicen dake karuwa da matsalar sauyin yanayi, da talauci, da yunwa da karuwar rashin daidaito da son zuciya, wariyar launin fata da karuwar kalaman nuna kiyayya da tsarin kudi na duniya da ya zugura dabi’u da haifar da talauci da tarzoma ga kasashe masu tasowa.

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su agazawa kasashe masu tasowa, yayin da suke gina ababan more rayuwa masu inganci a kokarin kare daukacin al’umma daga tasirin sauyin yanayi, domin tabbatar da kiyaye hakki da martabar dukkan jama’a, da daukar managartan matakai na hadin gwiwa da gano mabambantan al’adu, da addinai da al’ummomi daban-daban a matsayin albarka maimakon wata barazana. (Ibrahim)