logo

HAUSA

Shugaban Indonesia ya bayar da umarnin gudanar da bincike game da turmutsitsin da ya faru a filin wasan kwallon kafan da ya halaka mutane 174

2022-10-02 16:01:15 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo, ya umarci ‘yan sanda Lahadi nan, da su gudanar da bincke, game da turmutsitsin da ya faru a filin wasan kwallon kafa, wanda ya zuwa yammacin Lahadi ya yi sanadiyar mutuwar mutane 174 tare da jikkatar wanu kimanin 180, bayan kammala wani wasan kwallon kafa.

Shugaban ya kuma umarci hukumar wasan kwallon kafa ta kasar (PSSI) da ta dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a kasar dake kudu maso gabashin Asiya na wani dan lokaci, har sai an kammala binciken musabbin turmutsitsin da ya faru.

Bayanai na cewa, ‘yan sanda biyu na daga cikin wadanda suka mutu a lamarin. Abin da ya faru, daya daga cikin mummunan bala’i da suka faru a filin wasa a duniya, ya faru ne a daren ranar Asabar a filin wasa na Kanjuruhan dake Malang na lardin gabashin Java dake kasar ta Indonesia, bayan da kungiyar wasan kwallon kafa ta Arema Malang ta sha kashi a hannun kungiyar Persebaya Surabaya a wasan gasar kwallon kafan kasar.

Kafofin watsa labaran cikin gida, sun ruwaito cewa, magoya bayan kungiyar da ta sha kashi a gida ne, suka haura katanga, inda suka shiga filin wasan kwallon kafan, lamarin da ya haifar da arangama da ‘yan sanda da kuma turmutsitsi.

Rahotanni na cewa, ‘yan sanda sun harba hayaki mai sa kwalla kan jama’a, lamarin da ya haifar da firgici tsakanin dandazon jama’a. Jama’a dai sun yi kokarin ficewa daga filin wasan, abin da ya haddasa turmutsitsi a kofar fita daga filin wasan.(Ibrahim)