logo

HAUSA

Amurka ta sanar da saka wani sabon zagayen takunkumai kan Rasha

2022-10-01 16:56:01 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da matakan takunkumai da ta sakawa kasar Rasha a jiya.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar da daukar matakan kayyade takardun visa na mutane 910 ciki har da sojojin kasar Rasha, da hafsoshin sojojin kasar Belarus. Ma’aikatar harkokin kudi ta kasar Amurka kuma, ta sanar da saka takunkumi ga mambobin kungiyar hadin gwiwar sojoji da masana’antu ta kasar Rasha, da shugaban babban bankin kasar da sauransu. Kana ma’aikatar kasuwancin kasar Amurka, ta sanar da shigar da kamfanoni 57 dake kasar Rasha da zirin Crimean, cikin jerin sunayen kamfanonin da suka saba wa ka’idojin fitar da kayayyaki na kasar.

A jiya ne, aka gudanar da bikin sa hannu kan yarjejeniyar shiga kawancen kasar Rasha da yankunan Donetsk, da Lugansk, da Kherson, da kuma Zaporizhzhia suka yi. (Zainab)