logo

HAUSA

Sin ta bukaci a komawa shawarwari domin warware batun zargin amfani da makamai masu guba a Syria

2022-09-30 12:49:07 CMG Hausa

Kasar Sin ta bukaci a komawa tattaunawa da shawarwari, domin warware batun zargin amfani da makamai masu guba a Syria.

Wakilin Sin, wani babban jami’in dake ofishin dindindin na wakilci dake MDD Sun Zhiqiang shi ne ya yi wannan kira a jiya Alhamis. Yana mai cewa rahoton da babban darakta na hukumar hana amfani da makamai masu guba ko OPCW ya fitar a watan jiya, ya nuna cewa, tsakanin ranakun 11 zuwa 18 ga wata, ofishin tsare-tsaren ayyukan OPCW, ya gudanar da zagaye 9 na binciken kwakwaf, a cibiyar binciken kimiyya ta Syria.

Sun, wanda ya bayyanawa zaman kwamitin tsaron MDD halin da ake ciki, don gane da batun amfani da makamai masu guba a Syria ya ce "Mun lura cewa, gwamnatin Syria da ofishin tsare-tsaren ayyukan OPCW, sun fara tuntubar juna da musaya, game da sakamakon binciken da aka gudanar."

Jami’in ya kuma yi kira ga ofishin tsare-tsaren ayyukan hukumar OPCW, da ya dora muhimmancin gaske, ga damuwar sassan masu ruwa da tsaki don gane da batun takardun VISA na shiga Syria, tare da fatan sassan biyu za su ci gaba da tattaunawa, game da shirin da ake yi na ganawa tsakanin babban daraktan OPCW da ministan wajen kasar ta Syria.  (Saminu Alhassan)