logo

HAUSA

Csaba Korosi: Sin ta zamo babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD

2022-09-30 12:36:18 CMG Hausa

Shugaban babban taron MDD na 77 Csaba Korosi ya bayyana cewa, kasar Sin a matsayin babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Mr. Korosi, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin taron taya murnar cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ofishin wakilcin Sin a MDD ya kira ta kafar bidiyo. Ya ce a matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka assasa MDD, kuma wakiliyar dindindin a kwamitin tsaron majalissar, Sin ta taka rawar gani yadda ya kamata.

Korosi ya kuma taya Sin murnar manyan nasarorin da ta cimma a fannin ingiza ci gaba da wadatuwar al’ummarta. Ya ce "Manufar kasar Sin ta ciyar da duniya gaba, na kunshe da damar ingiza samun ci gaba mai dorewa, da aiwatar da ajandar ci gaba ta MDD ta nan da shekarar 2030".

Taron da ofishin wakilcin na Sin a MDD ya kira, ya samu mahalarta kusan mutane 200, da suka hada da manyan jami’an MDD, da wakilan dindindin na kasashe daban daban, da manyan jami’an diflomasiyya daga sama da kasashe 100, da ’yan jarida daga kafofin watsa labarai na kasa da kasa da dama, da kuma aminan kasar Sin daga fannonin rayuwa daban daban. (Saminu Alhassan)