logo

HAUSA

Iraki ta zargi Iran da kaddamar da harin bam a yankin Kurdawa dake arewacin kasar

2022-09-29 15:48:09 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Iraki, ta bayar da sanarwa a jiya Laraba cewa, a wannan rana, Iran ta kaddamar da harin bam a yankin Kurdawa mai cin gashin kansa na arewacin Iraki, wanda ya haddasa mutuwar wasu mutane, kuma Irakin ta nuna matukar damuwa game da hakan, tare da alkawarin aiwatar da tsattsauran martanin diplomasiyya mafi girma.

Wata kafar watsa labarai ta Iran ta ce rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran, ta kai sabon hari kan sansanonin ‘yan ta’adda dake arewacin Iraki.

Bayan aukuwar lamari, wani ma’aikacin hukumar kiwon lafiya ta yankin na Kurdawan da ya ganewa idanun sa yanayin, ya ce harin bam da Iran ta kai a wannan karo, ya haddasa rasuwar mutane kusan 5, kuma fiye da 30 sun ji raunuka.

Kaza lika kafar watsa labarai ta “Kurdistan 24” ya ba da labari a shafin ta na Intanet cewa, mutane 9 sun mutu sakamakon aukuwar harin na bam.  (Safiyah Ma)