logo

HAUSA

Hukumar NDLEA ta lalata ton 1.8 na hodar ibilis da ta kwato

2022-09-28 10:40:45 CMG HAUSA

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, ta kona ton 1.8 na hodar ibilis da ta gano a baya-bayan nan, a wani gidan ajiya dake Lagos, cibiyar kasuwanci ta kasar.

Da yake jawabi yayin lalata hodar ibilis din, shugaban hukumar NDLEA, Mohammed Buba Marwa ya ce, bisa yawan hodar, darajarta a titi ya kai sama da dala miliyan 278, wanda ke bayyana zurfin ayyukan fataucin miyagun kwayoyi a bayan fage.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce a ranar 19 ga watan Satumba, jami’an hukumar suka yi wa wani gidan ajiya dake yankin Ikorodu na birnin Lagos tsinke, inda suka gano ton 1.8 na hodar ibilis tare da cafke wasu mutane 5. (Fa’iza Mustapha)