logo

HAUSA

Ambaliya ta yi sanadin mutuwar mutane 23 da raba wasu 116,000 da muhallansu a yankin tsakiyar Nijeriya

2022-09-28 10:41:54 CMG HAUSA

 

Mutane a kalla 23 ne suka mutu, wasu sama da 116,000 kuma sun rasa muhallansu sanadiyyar ambaliya ruwa a jihar Benue dake tsakiyar kasar Najeriya.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Emmanuel Shior, ya shaidawa manema labarai a birnin Makurdi cewa, ambaliyar ruwa ta haifar da asara a jihar, tun bayan shiga lokacin damina a watan Mayun bana.

Ya ce mutane 116,084 ne suka rasa matsugunansu yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye yankunan kananan hukumomi 11. Yana mai cewa lamarin ya shafi jimilar iyalai 12,856.

Ya kara da cewa, mutane na bukatar agajin gaggawa. Kuma kawo yanzu, ambaliyar ta lakume kadada 14,040 na gonaki da gidaje 4,411 a fadin jihar. Har ila yau, ta shafi makarantu da kasuwanni da kamfanoni da gidaje da gonaki a yankuna 104.

A jiya Talata, hukumar kula da agajin gaggawa ta jihar ta fara aikin rabon kayayyakin tallafi a fadin jihar, ga wadanda lamarin ya rutsa da su a birnin Makurdi, da nufin tallafawa dukkan wadanda lamarin ya shafa. (Fa’iza Mustapha)