logo

HAUSA

An gudanar da bikin nune-nunen masanan’antun nukiliya na Sin a ofishin MDD dake Vienna

2022-09-28 11:28:58 CMG HAUSA

 

An bude bikin nune-nunen masanan’antun nukiliya na Sin mai taken “nukiliya ta kira makoma” wanda zai gudana daga ranar 26 ga watan Satumba zuwa ranar 30 ga wata, a ofishin MDD dake Vienna na Austria. A jiya Talata, wakilin Sin dake Vienna Wang Qun da babban direktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi sun halarci bikin nune-nunen tare, yayin da suka halarci taro karo na 66 na hukumar makamashin nukiliya ta duniya.

Hukumar makamashin nukiliya ta kasar Sin ce ta dauki nauyin tsara nune-nunen, kuma kamfanin nukiliya na kasar Sin ne ya dauki nauyin gudanar da bikin. Yayin nune-nunen, za a yi nune-nunen nasarorin da Sin ta samu ta hanyar amfani da nukiliya lami lafiya, da kuma gudummawar da Sin ta bayar a fannonin inganta ci gaban nukiliya ta duniya da kyautata yanayin duniya da gina gidaje masu kyau da dai sauransu. (Safiyah Ma)