logo

HAUSA

Sin ta yi kira a daidaita batun Ukraine ta hanyar siyasa

2022-09-28 10:09:44 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi yayin da kwamitin sulhu na majalisar yake nazarin batun kasar Ukraine jiya Talata, inda ya yi kirayi ga kasa da kasa da su daidaita batun ta hanyar siyasa.

Zhang Jun ya bayyana cewa, kasar Sin ta lura da sabon sauyin dake faruwa a Ukraine, kuma ta saurari ra’ayoyin da bangarori daban daban da abin ya shafa suka bayyana kan batun, don haka tana ganin cewa, ya dace a martaba ikon mulkin kasa, da cikakken yankin kasa, da ka’idojin MDD. Haka kuma, kamata ya yi a goyi bayan kokarin da ake yi domin daidaita rikici cikin lumana. Ya ce a ko da yaushe, kasar Sin tana nacewa kan manufar wanzar da zaman lafiya, kuma za ta ci gaba da ba da gudummowarta a bangaren. (Jamila)