logo

HAUSA

Babban zauren MDD ya kammala zaman muhawara na bana

2022-09-27 11:49:59 CMG Hausa

An kammala muhawarar babban taron MDD na bana, bayan da mambobi wakilan kasashe 190 suka yi jawabi bisa taken "Lokaci mai cike da sarkakiya: hanyoyin kawo sauyi ga kalubalen da suka dabaibaye juna."

Shugaban babban taron MDD karo na 77 Csaba Korosi, ya bayyana a jawabinsa na rufe taron cewa, shugabannin kasashe da gwamnatoci 126 ne suka halarci muhawarar ta bana. Yana mai cewa, ya samu sakonni biyar daga mambobin kasashe a yayin babbar muhawarar.

Na farko shi ne kara wayar da kan jama'a su fahimci cewa, dan Adam ya shiga wani sabon zamani, Sako na biyu shi ne, ya kamata a kawo karshen rikicin kasar Ukraine. Na uku shi ne, sauyin yanayi yana lalata bil-adama sannu a hankali. Na hudu, kira domin a inganta yanayin hakkin dan Adam da kuma biyan bukatun wadanda suka fi fuskantar cin zarafi.

Batu na biyar a cewar sa, shi ne wanda ake goyon bayan sa matuka, wato zamanantar da MDD, da farfado da babban taron da kuma yi wa kwamitin sulhun majalisar gyaran fuska.

Muhawarar gama-gari ta bana, ita ce ta farko tun bayan bullar cutar COVID-19, inda aka bukaci shugabannin kasashen duniya da su bayyana ra’ayoyinsu da bakinsu a zauren taron. (Ibrahim)