logo

HAUSA

Yawan bakin hauren da suka mutu a cikin kwale-kwalen da ya nutse a teku ya karu zuwa 102

2022-09-26 10:32:24 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 102, bayan da wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya kife a gabar tekun Syria, yayin da wasu 40 kuma suka bace.

kungiyar dake sanya ido kan kare hakkin dan Adam ta kasar Syria wato Syrian Observatory for Human Rights, ta bayyana cewa, hukumomin kasar sun yi nasarar ceto mutane 20.

Wata sanarwa da mahakuntan kasar suka fitar ta bayyana cewa, kwale-kwalen mai dauke da bakin haure kusan 150, ya taso ne daga kasar Lebanon a ranar Talata, a kan hanyarsa ta zuwa nahiyar Turai. Ya kuma nutse a kusa da gabar tekun Tartous dake gabar ruwan Syria a ranar Alhamis.

Bayanai na cewa, bakin hauren 'yan kasashen Labanon da Siriyawa, da kuma Falasdinawa ne, wadanda ke kokarin tserewa wahalhalun rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki a yankunansu.

Wakilin musamman na MDD a kasar Syria Geir Pedersen, ya fada a jiya cewa, hadarin jirgin ruwan bakin hauren da ya afku a kusa da kasar Syria wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama yana da muni.

Pedersen ya bayyana cewa, akwai bukatar a kara kaimi wajen tunkarar tushen wadannan matsaloli, da suka hada da rikicin Syria da na tattalin arziki a kasar Labanon, da kuma kare wadanda ke da matukar rauni, ta yadda ba za a tilasta musu yin irin wadannan zabi na neman inganta rayuwa masu wahala da hadari ba. (Ibrahim Yaya)