logo

HAUSA

Rikici ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a yammacin Libya

2022-09-26 11:39:38 CMG Hausa

Tashar talabijin ta Al-Ahrar ta kasar Libya ta bayar da rahoton cewa, wani kazamin fada ya barke jiya tsakanin wasu kungiyoyi biyu masu dauke da makamai a birnin Zawiya dake yammacin kasar Libya, mai tazarar kilomita 45 daga yammacin Tripoli, babban birnin kasar.

Rahotanni na cewa, mutane da dama ne suka kwanta dama ko kuma suka jikkata sakamakon arangamar, inda aka yi amfani da matsakaita da manyan makamai.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Libya, ta yi kira da a gaggauta dakatar da fadan, domin a samu damar kwashe fararen hula da suka makale a yankunan dake kusa da yadda ake gwabza fadan, domin tsira da rayukansu. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance dangane da rikicin.

Rikici na baya-bayan nan na zuwa ne, bayan wani kazamin fada da aka yi a birnin Tripoli a tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai a karshen watan Agusta, inda aka kashe mutane fiye da 20 kana fiye da 140 kuma suka jikkata. (Ibrahim Yaya)