logo

HAUSA

Masar ta kaddamar da shirin koyar da Sinanci na gwaji a makarantun midil na kasar

2022-09-26 10:19:03 CMG Hausa

A jiha ne, aka shirya wani biki a kwalejin Confucius na jami'ar Alkahira dake kasar Masar, don kaddamar da wani shirin koyar da harshen Sinanci na gwaji a makarantun midil da kuma shirin horar da malaman kasar.

Jami'i mai kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar Zhang Tao, ya bayyana a cikin wani sakon bidiyo cewa, makarantun sakandaren gwamnatin Masar guda 12 ne za su shiga cikin shirin na gwaji, abin da ke zama wani sabon mafari na koyar da harshen Sinanci a makarantun midil na kasar.

Zhang ya bayyana cewa, a watan Satumba na shekarar 2020 ne, kasashen Sin da Masar suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, don koyar da harshen Sinanci a matsayin harshen waje na biyu na zabi a makarantun firamare da sakandare na Masar.

Ya kara da cewa, kasashen biyu sun kuma samu babban ci gaba a fannin hadin gwiwar makarantu, da koyar da sana'o'i, da hazikai, da kuma hadin gwiwa a fannin binciken kimiyya.

A nasa bangaren, mataimakin ministan ilimi da ilimin fasaha na Masar Mohamed Megahed, ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, kasashen Masar da Sin sun karfafa hadin gwiwarsu a fannin ilimi.

Ya kara da cewa, an yi nasarar kaddamar da shirin koyar da Sinanci na gwaji ne, shekara guda kafin lokacin da aka tsara, sakamakon kokarin hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi, yana mai fatan shirin zai taimaka wa Masirawa da dama kara fahimtar kasar Sin.

Shirin horar da malaman, zai dauki tsawon kwanaki 10, inda za a koyar da darussa game da hanyoyin koyarwa, da koyan harshe, da yadda za a yi amfani da ma sarrafa littattafai na yanar gizo. Malamai 12 ne za su fara aikin koyar da harshen Sinanci bayan kammala samun horon. (Ibrahim Yaya)