logo

HAUSA

Shugaban gwamnatin Jamus ya kai ziyara Qatar

2022-09-26 10:10:48 CMG Hausa

A yammacin jiya ne, sarki Tamim Bin Hamad Al Thani na kasar Qatar, ya tattauna da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, wanda ke ziyarar aiki a kasar, inda suka yi musanyar ra’ayi kan batun game da fitar da iskar gas zuwa Jamus da sauransu.

Scholz ya sauka birnin Doha, fadar mulkin Qatar ne a jiya, domin gudanar da ziyarar aiki ta yini daya a kasar. Yayin taron ganawa da manema labaran da suka kira bayan tattaunawarsu, sarki Tamim ya bayyana cewa, kamfanonin makamashi na kasashen biyu suna nazarin hanyoyin zuba jari a fannin makamashi, kuma Qatar ta kwashe shekaru tana kokarin fadada yawan samar da iskar gas ta arewacin kasar domin magance karuwar bukatar kasashen duniya ta iskar gas. Ya kara da cewa, yayin tattaunawarsu, sassan biyu sun bayyana cewa, ya dace a daidaita matsalolin dake shafar shiyya shiyya ko kasa da kasa ta hanyar yin tattaunawa da matakai na diplomasiyya.

A nasa bangare, Scholz ya bayyana cewa, kasar Jamus tana fatan kara shigo da iskar gas daga Qatar, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Qatar a fannonin samar da wutar lantarki, da jirga-jirgar jiragen sama, da raya sabbin fasahohin zamani, da kera manyan na’urorin masana’antu da sauransu.

Qatar dai ita ce zango na uku na ziyarar Scholz a yankin tekun Fasha a wannan karo, bayan da ya ziyarci kasar Saudiyya da hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya nemi samar da makamashi a matsayin daya daga cikin manyan dalilai na ziyarar tasa. (Jamila)