logo

HAUSA

Iran ta bayyana takaici dangane da matakin gwamnatin Ukraine na rage darajar huldar dake tsakaninsu

2022-09-25 16:36:22 CMG Hausa

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Nasser Kanani, ya bayyana takaici dangane da matakin da gwamnatin kasar Ukraine ta dauka na rage darajar huldar diflomasiyya tsakaninta da Iran.

A ranar Juma’a ne, Ukraine ta sanar da rage darajar huldarta da Iran, tare da kin amincewa da takardar nadin jakadan Iran a kasar, bisa abun da ta kira da matakin da ya sabawa tsarin abota, wanda Iran ta dauka, na samarwa kasar Rasha jirage marasa matuka da za a yi amfani da su wajen kai wa dakaru da al’ummarta hari.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, gwamnatin Ukraine ta dauki matakin ne bisa dogaro da rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, wadanda wasu kasashen waje suka kitsa, sannan kafofin watsa labarai ke yayatawa.

Kakakin ya kuma shawarci Ukraine da kada ta biyewa wasu daga waje dake neman bata dangantakarta da Iran.

Bugu da kari, ya ce dangane da rikicin Rasha da Ukraine, Iran ba ta dauki wani bangare don goya masa baya ba, kuma ta bayyana matsayinta na adawa da yaki da bukatar warware rikicin a siyasance.

Ya kuma jaddada cewa, Iran za ta mayar da martani daidai da matakin da Ukraine ta dauka. (Fa’iza Mustapha)