logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci muhawarar babban taron MDD karo na 77

2022-09-25 17:02:15 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci muhawarar babban taron MDD karo na 77 a hedkwatar majalisar dake birnin New York na kasar Amurka, tare da gabatar da jawabi mai taken “Yin kokari don samun ci gaba cikin lumana da kuma daukar alhaki don samun ci gaba ta hanyar hadin gwiwa”.

Wang Yi ya bayyana cewa, wannan zamani na cike da kalubale da kyakkyawan fata. Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar bisa bukatun zamanin da ake ciki.

Ya ce ya kamata a kiyaye zaman lafiya, da magance yake-yake. Kana Sin tana son daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.

Ya kara da cewa, ya kamata a samu ci gaba a fannin yaki da talauci. Yana mai cewa, Sin tana daukar aikin samun ci gaba a matsayin muhimmin aiki na ajandar tattaunawa ta kasa da kasa, don neman samun daidaito daga kasa da kasa, ta yadda nasarorin da aka samu za su amfanawa kowace kasa da jama’arta.

Wang Yi ya ci gaba da cewa, ya kamata a bude kofa ga kasashen waje. A yi shawarwari don magance tada rikice-rikice, da kin amincewa da tafiyar da harkokin siyasa a cikin kungiyoyi da kuma nuna kiyayya da juna a cikin kungiyoyi daban daban.

Bugu da kari, ya kamata a yi hadin gwiwa da juna, a yi watsi da kiyayya. Ya ce bai kamata a bambanta ra’ayoyi domin bambancin tsarin kasa ba, yana mai cewa, kamata a yi hadin gwiwa da juna don sa kaimi ga samun zaman lafiya da ci gaba tare.

A karshe, ya ce kamata ya yi a tabbatar da adalci ga juna. A aiwatar da ra’ayin bangarori daban daban, da sa kaimi ga kasa da kasa su samu adalci a fannonin kare hakki, da ka’idoji, da samun dama, da kuma kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasa da kasa bisa girmamawa juna da adalci da hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna. (Zainab)