logo

HAUSA

Masar na fatan samun kyakkyawan sakamako yayin taron sauyin yanayi da za a yi a watan Nuwamba

2022-09-25 16:18:32 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry, ya yi kira da a yi kokarin tabbatar da samun kyakkyawan sakamako yayin taron sauyin yanayi na MDD ko COP27, wanda zai gudana cikin watan Nuwamba a Masar din.

Ya ce a mastayinta na mai karbar bakunci taron, Masar na kira ga dukkan wadanda suka shiga cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta COP27, su cika alkawurran da suka dauka, su kuma tallafawa kasashe masu tasowa da kasashe matalauta a kokarin da suke yi na tunkarar mummunan tasirin sauyin yanayi.

Sameh Shoukry ya ce wadannan kasashe su ne suka fi bukatar taimako bisa la’akari da ka’idar daidaito da buri na bai daya da mabambantan hakkoki.

Ya kara da cewa, damar samun ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris, musammam takaita dumamar yanayi, na da nasaba sosai da sakamako masu karfi da za a samu daga taron da za a yi a Sharm El-Sheikh, yana mai cewa, Masar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen samar da yanayi mai kyau da ake bukata na samun kyawawan sakamako. (Fa’iza Mustapha)