logo

HAUSA

Ministan wajen kasar Sin ya halarci taron ministocin BRICS

2022-09-24 16:39:15 CMG Hausa

A ranar Alhamis ne babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin kungiyar BRICS, a gefen babban taron MDD karo na 77, dake gudana a birnin New York na Amurka.

Da yake tsokaci yayin taron, Wang Yi ya ce a watan Yunin bana, an gudanar da taron shugabannin kungiyar BRICS karo na 14 cikin nasara, wanda kuma ya ba da damar bude sabon fagen hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar. Ya ce a yanzu haka, yanayin harkokin duniya na cike da rashin tabbas da sarkakiya, yayin da kalubale daban daban ke ci gaba da fuskantar sassan kasa da kasa. Wang Yi ya kara da cewa, tsaro shi ne jigon ci gaba, yayin da kuma ci gaba ke tabbatar da tsaro.

A cewar sa, kamata ya yi kasashe mambobin kungiyar BRICS su mara baya sosai, ga fannonin da ka iya ingiza ci gaba, yayin da suke halartar babban taron MDD, su kuma shigar da sabon kuzari ga ayyukan dake cikin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD, ta nan da shekarar 2030. Kaza lika ya kamata a yi watsi da duk wata manufa ta rarrabuwa, da warewa, da shingayen fasahohi, maimakon hakan a tabbatar da gina budadden tattalin arzikin duniya, domin cimma nasarar bunkasar duniya tare, da kare muhalli da kare lafiyar al’umma.

Wang Yi ya kuma bayyana cewa, taron kungiyar G20 na Bali na karatowa, don haka ya kamata a karfafa tuntubar juna, da kyautata tsare tsare don kare halastaccen hakki, da moriyar kasashe masu samun saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa. Bugu da kari, ya dace a bibiyi managartan tsare tsaren da shugabannin kungiyar BRICS suka samar, a aiwatar da sakamakon taron, a cimma matsaya guda, da rungumar karfin hali irin na kungiyar BRICS. (Saminu Alhassan)