logo

HAUSA

Sin tana son ci gaba da fadada yankunan hadin gwiwa da kasashen Asiya da na Turai don samun ingantaccen ci gaba tare

2022-09-23 21:00:50 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi karin haske kan bikin baje koli na Sin da Asiya da Turai karo na 7, a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Jumma’a, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashe daban daban, wajen yin amfani da bikin baje kolin, don ci gaba da fadada fannonin hadin gwiwa tsakanin Asiya da Turai, da inganta matsayin hadin gwiwa a tsakaninsu, da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwa da wadata tare.

A cewar Wang Wenbin, daga ranar 19 zuwa 22 ga wata, an gudanar da baje koli na Sin da Asiya da Turai karo na 7 a birnin Urumqi na jihar Xinjiang ta kasar Sin. Taken bikin baje kolin na bana shi ne "Tattaunawa tare kan manyan manufofin hadin kai, kafa dandalin hadin kai tare, da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kai, da kuma kafa makoma cikin hadin gwiwa ", wanda ya jawo jimillar kamfanoni 3,597 daga kasashe da yankuna 32 na duniya, wadanda suka halarci bikin baje kolin, da nuna kayayyakinsu ta yanar gizo, da kuma kamfanoni 2,652 wadanda suka nuna kayayyakin su ta yanar gizo.

Ya zuwa yanzu, wannan baje koli ya tattara ayyuka 448 da aka rattabawa hannu, kana da jimillar kudin da ya kai yuan tiriliyan 1.17, wanda ya kafa wani sabon matsayi ga bikin baje kolin Asiya da Turai na baya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)