logo

HAUSA

Dakarun kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya

2022-09-23 10:15:56 CMG HAUSA

 

Mataimakin sakatare janar na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix ya yabawa dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin bisa nasarorin da suka samu a ayyukan wanzar da zaman lafiya na majalisar.

Jean-Pierre Lacroix ya ce, dakarun suna taka muhimmiyar rawa tare da bayar da gudunmawa gaya wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Jami’in wanda ya zanta da wakilin kafar CMG yayin babban taron zauren MDD na 77 dake gudana a birnin New York, ya jaddada cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya na Sin sun gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankuna kamar na Gabas ta Tsakiya da Afrika, kana sun nuna sanin ya kamata irin na babbar kasa yayin da suke aikin.

A cewar wata takardar bayani mai taken “shekarun 30 da shigar sojojin kasar Sin cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD” da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar a shekarar 2020, sojojin kasar na nuna goyon baya mai karfi ga shirin wanzar da zaman lafiya na MDD na ko-ta-kwana. Yanzu haka, kasar Sin ta kammala wata rundunar shirin ko-ta-kwana dake kunshe da sojoji 8,000 da rukunoni 28 na kwararru a bangarori 10. Game da hakan, Jean-Pierre Lacroix ya ce kasar Sin ta bayar da gudunmawa ga zaman lafiyar duniya a aikace, kuma MDD za ta ci gaba da hada hannu da ita a harkoki masu ruwa da tsaki.

Yanzu haka, adadin dakarun kasar Sin shi ne mafi yawa cikin mambobin dindindin na kwamitin sulhu na MDD. Haka kuma, kasar ta shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya kusan 30, inda ta tura sama da dakaru 50,000. (Fa’iza Mustapha)