logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya bukaci Amurka da ta daina tsoma bakin soja ba bisa ka'ida ba a Syria

2022-09-23 10:53:12 CMG HAUSA

 

A yayin zaman taro na 51 na kwamitin kare hakkin dan-Adam, wakilin kasar Sin a kwamitin kare hakkin dan-Adam na MDD minista Jiang Duan ya yi Allah wadai da katsalandan din sojan da ya saba da doka da Amurka ta yi a kasar Syria. Mr. Jiang Duan ya nuna cewa, matakin soja na Amurka ya keta muhimman hakkokin bil-adama na al'ummar Syria, don haka, ya bukaci kasar Amurka da ta gaggauta dakatar da take hakkin bil-Adam da take yi.

Jiang Duan ya bayyana cewa, an shafe fiye da shekaru goma ana jinkirta batun kasar Syria, kuma har yanzu al'ummar kasar na fama da talauci da yaki. Kuma alhakin hakan ya rataya ne a wuyan Amurka da sauran kasashen yammacin duniya.

Kasar Amurka dai ta sha kaddamar da hare-haren soji a kasar Syria, lamarin da ya sabbaba hasarar rayukan fararen hula da matsugunai a Syria, tare da haddasa asarar dukiyoyi da ba za a iya misaltawa ba.

A watan da ya gabata ne sojojin Amurka suka kaddamar da wani sabon farmaki ta sama a gabashin kasar Syria, wanda ya ci gaba da keta hurumin kasar tare da kara ta’azzara wahalhalun da al’ummar Syria ke fama da shi.

Bugu da kari, kasar Amurka ta kakkaba wa kasar Syria wasu matakai na tilastawa, wadanda suka saba doka, lamarin da ya sa al'ummar kasar wahalar samun zaman lafiya na yau da kullum, kuma matakan raya tattalin arziki da sake gina kasar, duk suna fuskantar matsaloli.

Har zuwa wannan lokaci, sojojin kasar Amurka ne ke da iko kan rijiyoyin man fetur, da iskar gas da sauran albarkatun kasar, inda suka mamaye manyan yankunan kasar da ake hako mai, tare da kwashe sama da kashi 80 cikin 100 na yawan man da ake hakowa a kasar, suna kuma fasa kwauri da lalata hatsin da kasar Syria ta adana, hakan ya keta ’yancin al’ummar kasar na samun abinci, da lafiya, da bunkasuwa, da sauran muhimman hakkoki na bil-Adama matuka.

Jiang Duan ya ce, rikicin kasar Syria ya nuna cewa, tsoma baki na kasashen waje, da tsokana, da matsin lamba, da sanya takunkumai, ko kadan ba za su taimaka wajen warware matsalar ba. (Ibrahim Yaya)