logo

HAUSA

Guterres ya yi kira da a dauki managartan mataki don magance matsalolin yankin Sahel

2022-09-23 09:14:56 CMG HAUSA

 


Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira da a dauki matakan da suka wajaba don tinkarar matsalolin da suka addabi yankin Sahel.

Guterres ya shaidawa wani taron manyan shugabanni game da yankin Sahel da ya gudana a gefen makon babban zauren majalisar cewa, matsalar tsaro a yankin Sahel na barazana ga duniya baki daya, kuma idan har ba a dauki matakin da ya dace ba, to za a dandana illar ta'addanci, da tsattsauran ra'ayi da ma manyan laifuka fiye da yankin da ma nahiyar Afirka baki daya.

Ya ce, akwai bukatar kasashen duniya su gaggauta yin hadin gwiwa, kana wajibi ne mu sake yin tunani game da tsarin hadin gwiwa da kara yin tunani, fiye da kokarin da ake yi a halin yanzu.

A watan Disamba na shekarar 2021 ne, kungiyar tarayyar Afirka (AU) da MDD suka yi alkawarin yin aiki tare da kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka da G5 Sahel mai kunshe da kasashen Burkina Faso, da Chadi, da Mali, da Mauritania, da jamhuriyar Nijar, don inganta matakan tsaro a duniya, da tsarin gudanar da mulki da samun bunkasuwa a fadin yankin Sahel.

A wani bangare na wannan yunkuri, za a kaddamar da wani babban kwamiti mai zaman kansa, game da harkokin tsaro da ci gaba a yankin Sahel. Kwamitin wanda tsohon shugaban jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya jagoranta, zai gudanar da wani bincike mai zaman kansa, tare da bayar da shawarwari na musamman kan yadda za a magance tarin rikice-rikice da kuma tattara albarkatun da ake bukata, domin daukar matakan da suka dace kan wannan batu. (Ibrahim Yaya)