logo

HAUSA

Guterres ya bukaci a samar da isassun kudaden gudanar da ayyukan agajin yunwa a yankin Kahon Afirka

2022-09-22 10:14:26 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira da a samar da kudade ga dukkan ayyukan agaji a yankin kahon Afirka, yayin da matsalar yunwa ta mamaye yankin sakamakon fari.

A cikin wani sakon faifan bidiyo da ya aike a gyefen taron babban zauren majalisar kan bukatun gaggawa na jin kai a yankin kahon Afirka, babban jami'in majalisar ya bayyana cewa, miliyoyin mutane a kasashen Djibouti, da Eritriya, da Habasha, da Kenya da Somaliya, na fuskantar fari mafi muni da ba a taba ganin irinsa ba cikin kusan rabin karni. Don haka, ya yi kira da a dauki matakai uku cikin gaggawa don magance wannan matsala.

Na farko, samar da kudaden gudanar da duk wani nau'in matakan gaggawa, kama daga batun abinci, kula da lafiya da abinci mai gina jiki, har zuwa ga hidimomin samar da ruwa da tsaftar muhalli. Na biyu, tallafa wa kungiyoyin agaji na gida wadanda za su iya kaiwa ga mafiya rauni.

Na uku kuma na karshe, kira ga dukkan bangarorin dake rikici da juna, da su mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa, da kuma tabbatar da kaiwa ga mutanen da ke matukar bukata ba tare da wata matsala ba. (Ibrahim)