logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta aiwatar da kalaman shugaba Biden game da kaucewa cacar baka

2022-09-22 20:25:47 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi kira ga tsagin Amurka, da ya aiwatar da kalaman shugaban kasar Joe Biden, dangane da kauracewa barkewar sabuwar cacar baka, tare da fuskantar batun yankin Taiwan na kasar Sin bisa adalci.

A jiya Laraba, yayin taron MDD na 77 dake gudana a birnin New York, shugaba Biden ya jaddada matsayar gwamnatinsa, cewa ba ta da burin yin fito na fito da kasar Sin. Ya ce "Ba ma bukatar tashin hankali. Ba ma bukatar cacar baka. Ba ma bukatar wata kasa ta yi zabi tsakanin mu da wata kasa ta daban, ko wata abokiyar hulda".

Game da kalaman na shugaba Biden, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce abun lura shi ne shugaban na Amurka, ya sha furta irin wadannan kalamai a lokuta daban daban. Don haka fatan shi ne Amurka ta yi aiki tare da Sin, wajen zakulo dabarun zama tare bisa jituwa, tare da cimma moriyar juna, tsakanin manyan kasashen biyu dake da banbancin yanayin zamantakewa, da tarihi da al’adu.

Zhao ya kara da cewa, aiwatar da hakan zai amfani al’ummun Sin da na Amurka, kana zai ba da gudummawar wanzar da zaman lafiya, daidaito da ci gaban duniya baki daya.