logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci babban taron sauyin yanayi tare da gabatar da jawabi

2022-09-22 20:44:33 CMG Hausa

Jiya Laraba, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci babban taro kan sauyin yanayi a hedkwatar MDD dake birnin New York, inda kuma ya gabatar da jawabi.

Wang Yi ya ce, shugaba Xi Jinping ya tabbatar da cewa, duniya babban iyali ne, kuma dan Adam na da makomar bai daya, kana sauyin yanayi kalubale ne na gama-gari da ke bukatar hadin gwiwa. Kasar Sin na ganin cewa, ya kamata a sa kaimi ga cimma burin tafiyar da harkokin yanayin duniya a fannoni hudu.

Na farko shi ne mayar da hankali kan gudanar da taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Sharm el Sheikh.

Na biyu, a dora muhimmanci ga aiwatar da ayyuka. Ya kamata a dauki nauyin bai daya, amma tare da kiyaye bambancin sassa, da tsayawa kan ra’ayin bai daya da aka cimma, da kuma gaggauta aiwatar da burin da aka tsara a yarjejeniyar Paris.

Na uku kuma, a sa kaimi ga aiwatar da sauye-sauye ta hanyar kiyaye muhalli. Kana na hudu, a samar da kyakkyawan yanayi a fannin siyasa. Ya ce kamata ya yi kasashe masu ci gaba, su tabbatar da samun daidaito tsakanin yawan hayakin da a ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin, kafin shekarar 2060, wato lokacin da aka tsaida, da nufin samar da damar ci gaba ga kasashe masu tasowa, wanda hakan zai ba da damar sake gina amincewa juna, a tsakanin masu ci gaba da masu tasowa.

Kaza lika a dai wannan rana, Wang Yi ya kuma gana da firaministan kasar Georgia, da mai baiwa shugaban kasar Faransa shawara kan harkokin waje, da babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da tsaro, da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Norway, Hungary, Poland da kuma Somaliya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)