logo

HAUSA

Kasashe fiye da 30 sun nuna adawa ga takunkuman radin kai

2022-09-22 11:00:52 CMG HAUSA

 

Jiya Laraba ne, an shirya babban muhawara kan batutuwan da suka shafi ’yancin dan adam da suka hada da 'yancin tattalin arziki, da zamantakewa da al'adu da 'yancin samun bunkasuwa a yayin taron na 51 na kwamitin kare hakkin dan-adam na MDD.

Zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake Geneva, hedkwatar MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, Chen Xu ya gabatar da jawabi na hadin gwiwa a madadin kasashe fiye da 30, inda ya yi kira ga dukkan sassa, da su nace ga ruhin jama’a, ta yadda za a kara karfin ingiza kiyaye ’yancin tattalin arziki da al’umma da al’adu da kawar da rashin daidaito da nuna adawa a kan sanya takunkumin da ba shi da tushe a cikin dokokin duniya.

Wadannan kasashe fiye da 30 sun yi kira ga bangarori daban-daban da su mai da jama’a a gaban komai, ta yadda za su ci gajiyar ci gaba cikin adalci. Sun kuma yi kira da a mayar da hankali kan hadin kan kasa da kasa kamar yadda ke kunshe cikin ajandar samun ci gaba na MDD nan da shekarar 2030, ta yadda za a kokarta cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa guda 17 kamar yadda aka tsara.

Haka kuma ya kamata kwamiti da ofis mai kula da hakkin bil Adama da sauran kungiyoyi, su kiyaye ’yancin kasashe na zabar hanyoyin ci gaban kansu da kansu, da kuma nuna adawa ga tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, da kin amincewa da sanya takunkumi na kashin kai da suka sabawa dokokin kasa da kasa, da nuna rashin jin dadi kan siyasantar da ’yancin samun bunkasuwa. (Amina Xu)