logo

HAUSA

Fasahar nukiliya ta Sin ta fi mayar da hankali wajen amfanawa rayuwar al’umma

2022-09-22 10:39:45 CMG Hausa

Hukumar kula da makamashin nukuliya ta kasar Sin (CAEA) ta ce cikin shekarun baya-bayan nan, kasar ta yi amfani da fasahar nukiliya a bangarori da dama na tattalin arzikinta, lamarin da ya amfanawa rayuwar al’umma.

Sama da kwararru da malamai 90 ne suka hadu a taron hukumar CAEA na jiya, domin tattauna amfanin fasahar nukiliya ga rayuwar al’umma da yanayin da ake ciki yanzu da kuma shawarwarin yadda za a yi amfani da fasahar a nan gaba a kasar Sin.

A cewar Dong Baotong, mataimakin daraktan hukuma CAEA, ana amfani da fasahar nukiliyar a fannoni da dama kamar na masana’antu da aikin gona da kiwon lafiya da kare muhalli da tsaro.

Taron ya gabatar da muhimman shirye-shirye 10, domin nuna sakamakon da aka samu daga amfani da fasahar a bangaren tattalin arzikin kasar a baya-bayan nan. An samu galibin sakamakon ne a bangaren kiwon lafiya, kamar fasahar Heavy-ion ta farko da Sin ta yi amfani da ita wajen maganin cutar daji. (Fa’iza Mustapha)