logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon murna ga bikin tunawa da ranar zaman lafiya ta kasa da kasa

2022-09-21 20:50:36 CMG Hausa

An yi bikin tunawa da ranar zaman lafiya ta kasa da kasa ta bana a yau Laraba a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, bikin da ya samu sakon murna daga shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Xi ya bayyana cewa, yanayin tsaron duniya na fuskantar manyan sauye-sauye a halin yanzu, kuma duniya ta shiga wani sabon lokaci na sauye-sauye, inda ya fitar da shawarar tsaron duk duniya, da yin kira ga kasa da kasa, da su tsaya ga ra’ayin tsaro na bai daya, cikin hadin-gwiwa kuma mai dorewa, da mutunta ‘yancin kai, da cikakkun yankuna na kowace kasa, da girmama kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, da maida hankali kan damuwar kasa da kasa.

Haka kuma, Xi ya yi kira a daidaita rikici da sabanin ra’ayi tsakanin kasashe ta hanyar yin shawarwari, da daukar nauyin shimfida zaman lafiya, da bin tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, a wani kokari na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)