logo

HAUSA

An kaddamar da muhawara a babban zauren MDD

2022-09-21 11:01:48 CMG Hausa

An kaddamar da taron muhawara a babban zauren MDD na 77, a hedkwatar majalisar dake birnin New York na kasar Amurka, a jiya Talata. Inda shugabanni, da manyan kusoshin kasashe daban daban, za su tattauna matakan da za a iya dauka, don tinkarar manyan batutuwa da kalubalolin da ake fuskanta a duniyarmu, wadanda suka hada da yanayin da ake ciki a kasar Ukraine, da sauyin yanayin duniya, da annobar COVID-19, gami da yadda za a kula da wasu manyan batutuwan da ke janyo hankalin gamayyar kasa da kasa, irinsu raya tattalin arzikin kasashe daban daban, da yin gyaran-bawul kan tsare-tsaren MDD, da dai makamantansu.

Yayin da yake sanar da kaddamar da taron, Antonio Guterres, babban magatakardan MDD, ya yi kira ga kasashe daban daban, da su nuna goyon baya ga majalisar, ta yadda za ta sauke nauyin dake bisa wuyanta na tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya. Ban da wannan kuma, ya bukace da su girmama dokokin kasa da kasa, sa’an nan su yi kokarin daidaita mabambantan ra’ayoyinsu ta hanyar shawarwari. (Bello Wang)