logo

HAUSA

Amina Mohamed: kasar Sin abin koyi ne a fannin yakar talauci

2022-09-21 11:08:36 CMG Hausa

Yayin da ake gudanar da babban taron MDD karo na 77 a birnin New York na kasar Amurka, wakilin CMG ya yi hira da Madam Amina Mohamed, mataimakiyar babban sakataren MDD, a ranar 19 ga wata. Inda babbar jami’ar ta yaba wa kasar ta Sin bisa gudunmowar da ta samar a kokarin cimma burin tabbatar da rage talauci a duniya, da MDD ta sanya a gaba. A cewarta kasar Sin abin koyi ne ga sauran kasashe, musamman ma a wannan fanni.

Madam Amina ta kara da cewa, za a amfana sosai ta hanyar koyi da dabarun kasar Sin. Kana a nata bangare, MDD za ta raba fasahohi masu kyau na kasar Sin ga kasashe daban daban, da tabbatar da ganin an kawar da talauci a duniya, domin cimma buri na farko na muradun ci gaba mai dorewa guda 17, wato kawar da talauci.

Yayin zantawar, jami’ar ta ce abubuwan da za su taka muhimmiyar rawa a kokarin fitar da jama’a daga kangin talauci a wurare daban daban, su ne aikin ba da ilimi, da samar wa mutane abinci mai gina jiki. Wadannan fannoni 2, in ji jami’ar, su ne manyan dalilan da suka sa kasar Sin cimma nasara a kokarin kawar da talauci. (Bello Wang)