logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin karfafa rundunar sojojin kasar ta yin amfani da kwarewar da aka samu daga gyare-gyare

2022-09-21 21:30:34 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin karfafa rundunar sojojin kasar ta yin amfani da kwarewar da aka samu daga gudanar da gyare-gyare kan harkokin tsaro da rundunar sojojin kasar.

Shugaba Xi, ya gabatar da bukatar hakan ne yayin wani taron karawa juna sani, game da batun gudanar da gyare gyare ga harkokin tsaro da rundunar sojin kasar Sin, wanda ya gudana a Larabar nan a birnin Beijing.  (Saminu Alhassan)