logo

HAUSA

Sin: An kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi

2022-09-21 10:58:17 CMG Hausa

Alkaluman da ma’aikatar aikin gona da raya kauyuka ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, zuwa yanzu an kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi na lokacin kaka a kasar.

Yawan gonakin hatsi da aka girbe ya kai fiye da kadada miliyan 15.7, jimillar da ta kai kashi 18.1% na daukacin gonakin hatsi dake kasar. An bayyana cewa, yadda ake girbin hatsin cikin sauri, ya karu da kaso 0.9, idan an kwatanta da na bara.

A dangane da yadda ake gudanar da aikin girbin hatsi a wurare daban daban na kasar kuwa, ya zuwa yanzu an riga an kammala rabin aikin girbi a yankin kudu maso yammacin kasar. Yayin da a wuraren dake dab da kogin Yangtse, da kuma kudancin kasar, an girbe kaso 25 na hatsin da aka shuka. A yayin da ake kokarin gudanar da aikin a sauran sassan kasar. Haka zalika, ana hasashen cewa, za a yi amfani da na’urori da injunan aikin gona kimanin miliyan 30 a wannan lokacin kaka, don tabbatar da cewa, an gudanar da aikin girbin hatsi kamar yadda aka tsara. (Bello Wang)