logo

HAUSA

Guterres ya yi kira da a hada kai don tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta

2022-09-21 10:17:51 CMG HAUSA

 

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana a jiya Talata cewa, duniya na cikin babbar matsala, kuma tana bukatar daukar matakin hadin gwiwa a dukkan bangarori.

Ya kuma yi gargadin cewa, kasashen duniya na cikin tabarbarewar al'amura a duniya, kuma ba su shirya ko daura aniyar tinkarar manyan kalubalen zamanin da muke ciki ba.

Ya ce, tashe-tashen hankula kamar rikicin kasar Ukraine, da matsalar sauyin yanayi da asarar nau’o’in halittu, da matsanancin yanayi na harkoki kudi da kasashe masu tasowa ke ciki, suna barazana ga makomar bil-adama da duniya baki daya, duk da ci gaban da ake samu a wadannan batutuwa da sauransu.

Ya kara da cewa, hatta kungiyoyi daban-daban da wasu kasashen duniya suka kafa a wajen tsarin hada-hadar kudi, sun fada cikin tarkon rarrabuwar kawuna, kamar kungiyar G20.

Don haka, tilsa ne wannan gamayyar ta kasashen duniya ta gaggauta kawar da rarrabuwar kawuna, tare da yin aiki tare, wadda ta fara da ainihin manufar MDD, wato samarwa da kuma dorewar zaman lafiya. (Ibrahim Yaya)