logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta maida martani kan sanya kamfanonin sadarwar Sin cikin takardar wadanda ke kawo barazana ga tsaron kasa da Amurka ta yi

2022-09-21 21:34:52 CMG Hausa

Kwamitin kula da harkokin sadarwa na kasar Amurka ya sanya kamfanonin sadarwar kasar Sin, ciki jerin kamfanonin dake kawo barazana ga tsaron Amurka. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a yau Laraba cewa, wannan wani yunkuri ne na daban, da Amurka ta yi, na matsawa kamfanonin kasar Sin ba gaira ba dalili, bisa hujjar tsaron kasa kawai. (Murtala Zhang)