logo

HAUSA

Wakilin Sin ya zargi kan yadda Amurka ke tsare mutane ba bisa doka ba

2022-09-21 16:11:26 CMG HAUSA

 

Wakilin kasar Sin ya zargi kan yadda ake tsare mutane ba bisa doka ba a Amurka a yayin taron yin musayar ra’ayoyi da kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 51 da hukumar kula da batun tsare mutane ba bisa doka ba suka shirya tare a ranar 19 ga wata.

Wakilin Sin ya bayyana cewa, a shekarar 2021, Amurka ta tsare bakin haure sama da miliyan 1.7, kuma a ciki akwai 80%, ciki har da yara dubu 45 da aka tsare su a gidajen yari masu zaman kansu. Bugu da kari, yanayin irin wadannan gidajen yari masu zaman kansu, ba su da kyau. Sakamakon haka, an lalata lafiyar mutanen da aka tsare, har ma a kan samu matsalolin take hakkin bil-adam a kullum a wadannan gidajen yari masu zaman kansu.

Haka kuma, a mafakar Brisburgh kadai, an tsare yara kusan 5000. A cikin shekaru 20 da suka gabata, har yanzu Amurka tana tsare da mutanen da ba a hukunta su bisa doka ba a kurkukun Guantanamo.

Sabo da haka, a watan Janairun bana, kungiyar kwararru ta musamman ta fitar da wata sanarwa inda ta nuna cewa, kurkukun Guantanamo ya kasance kamar wani “Tabo dake kan alkawarin da gwamnatin Amurka ta dauka na tafiyar da mulki bisa doka”. Kungiyar ta kuma nemi gwamnatin Amurka da ta kawo karshen “mummunan babi na cin zarafin hakkin dan Adam kamar yadda take so”.

Bangaren Sin ya bukaci Amurka da ta sanya idonta kamar yadda ya kamata kan matsalolin take hakkin bil Adama da suke faruwa a kasar Amurka, ta dakatar da tsare ’yan gudun hijira ba bisa doka ba da sauran al’amuran cin zarafin hakkin dan Adam. Haka kuma ya kamata ta biya kudin tallafi da ma diyya ga wadanda aka take hakkinsu. (Safiyah Ma)