logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Iran ya bukaci Amurka da ta kawo karshen ta'addancin tattalin arziki kan Iraniyawa

2022-09-21 11:20:29 CMG HAUSA

 

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya bukaci Amurka da ta kawar da ta'addancin tattalin arzikin da ta sanyawa Iraniyawa, maimakon shaguben da take yi kan mutuwar wata 'yar kasar ta Iran.

Amir-Abdollahian ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tiwita, a matsayin martani ga damuwar da Amurkar ta nuna game da mutuwar Mahsa Amini, 'yar shekaru 22 da haihuwa a hannun 'yan sanda a Iran. Yana mai cewa, an fara gudanar da bincike kan mutuwarta.

Amini dai ta mutu ne a wani asibiti, bayan da ’yan sanda suka tsare ta a birnin Tehran, lamarin da ya janyo fushin jama’a da tausayawa tsakanin al’ummar Iran.

Mashawarcin shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, Amurka za ta ci gaba da dorawa jami'an Iran laifi kan irin wannan cin zarafi. Sai dai a martanin da ya mayarwa Amurka, Amir-Abdollahian ya bayyana cewa, jami'an Amurkar suna amfani da batun 'yancin dan adam a matsayin wani makami kan abokan gaba.

 

Ya ce, a maimakon yin shagube ko yin kukan kada, tilas ne Amurka ta kawo karshen ta'addancin tattalin arzikin da ta sanya kan Iraniyawa. (Ibrahim)