logo

HAUSA

Fannin jigilar kaya na samun karuwa a kasar Sin

2022-09-20 11:09:23 CMG Hausa

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, aikin jigilar kayayyaki a nan kasar Sin na samun karuwa, inda a jiya Litinin, yawan motocin dakon kaya da suka bi tagwayen hanyoyin kasar ya kai fiye da miliyan 7 da dubu 689, jimillar da ta karu da kaso 11.43 bisa ta watan da ya gabata.

Ofishin kula da aikin jigilar kayayyaki dake karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya gabatar da alkaluman, wadanda suka nuna cewa, a jiya 19 ga wata, jiragen kasa sun kwashe kayayyakin da nauyinsu ya kai ton miliyan 11 da dubu 125 a kasar, kana yawan kayayyakin da suka bi ta tashohin jiragen ruwa daban daban da aka gudanar da bincike a kansu ya kai ton miliyan 33 da dubu 213.

A fannin jiragen sama masu dakon kaya kuma, an samu zirga-zirgar jiragen sama guda 501 a kasar a jiya Litinin, inda daga cikinsu akwai jiragen sama 362 da suka yi jigilar kayayyaki zuwa kasashen ketare.

Ban da wannan kuma, kamfanoni masu jigilar kayayyaki cikin sauri na kasar Sin baki daya sun karbi kunshi kimanin miliyan 337 a jiya Litinin, yayin da yawan kayayyakin da suka kai wajen da ake neman tura su ya kai kimanin miliyan 312. (Bello Wang)