logo

HAUSA

Kasar Sin za ta fadada bude kofarta

2022-09-20 21:38:34 CMG Hausa

Kwanan nan ne hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bullo da jerin wasu rahotanni, dangane da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma, tun bayan da ta shirya babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis. Kididdigar ta yi nuni da cewa, daga shekara ta 2013 zuwa ta 2021, matsakaicin karuwar GDPn kasar a kowace shekara, yana karuwa da kaso 6.6 bisa dari, adadin da ya zarce na sauran sassan duniya, wato kaso 2.6 bisa dari, da irin sa na kasashe masu tasowa, wato kaso 3.7 bisa dari.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin ya bayyana a yau Talata cewa, a cikin jerin shekaru 10, yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ya zarce kaso 30 bisa dari, wanda ke kan gaba a duniya. Wannan abu ya shaida cewa, Sin kasa ce dake bayar da babban taimako ga habakar tattalin arzikin duniya. Wang ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje a nan gaba. (Murtala Zhang)