logo

HAUSA

An gudanar da jana’izar sarauniyar Ingila Elizabeth II

2022-09-19 20:46:33 CMG Hausa

Dubun dubatar mutane ne suka yi dandazo a kan titunan birnin London, yayin da ake gudanar da jana’izar ban kwana da marigayiya sarauniyar Ingila Elizabeth II, a kasaitaccen bikin da ake hasashen biliyoyin al’ummun duniya za su kalla ta akwatunan talabijin.

Sama da baki 2,000 aka gayyata, domin halartar jana’izar sarauniyar, ciki har da yariman masarautar Kuwait, Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah, da kuma manyan shugabannin kasashen duniya da suka hada da shugaban Amurka Joe Biden, da babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg. Sauran sun hada da mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, da shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Sarauniya Elizabeth II, ta rasu a ranar 8 ga watan nan na Satumbar nan, tana da shekaru 96 a duniya, a gidan sarauta dake yankin Scotland. Ita ce kuma sarauniya mafi dadewa a karagar mulkin masarautar ta Birtaniya.  (Saminu Alhassan)