logo

HAUSA

An kammala aikin girbin hatsi a gonakin fiye da kadada 11,333,333 na kasar Sin a wannan lokacin kaka

2022-09-19 14:01:24 CMG Hausa

Ma'aikatar aikin gona da kauyuka ta kasar Sin ta sanar a kwanan baya cewa, an riga an kammala aikin girbin hatsi a gonaki fiye da kadada 11,333,333 a kasar Sin, jamillar da ta kai kashi 13.3% na daukacin gonakin kasar da ake noman hatsi a ciki, a wannan lokacin kaka.

Ban da wannan kuma, wakilin CMG ya lura da muhimmiyar rawar da inshorar aikin gona ke takawa a fannin tabbatar da samun girbi mai armashi, inda kamfanonin inshora suke ba da tallafi ga manoma wajen tinkarar bala'i daga indallahi. Sa'an nan a lokacin da manoma suka samu hasara sakamakon iftila'i, kamfanonin za su biya su diyya. (Bello Wang)