logo

HAUSA

Shugaba Xi ya aike da wasikar taya murnar bude taron dandalin kasa da kasa a fannin samar da kayayyakin masana’antu

2022-09-19 19:41:21 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murnar bude taron dandalin kasa da kasa a fannin tabbatar da juriya da dorewar tsarin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni.

Xi Jinping ya aike da wasikar ne a Litinin din nan, ga mahalarta taron dandalin da aka bude a birnin Hangzhou, fadar mulkin lardin Zhejiang na kasar Sin.

Cikin wasikar tasa, shugaba Xi ya ce wanzar da juriya da daidaito a fannin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, hanya ce ta tabbatar da ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, tare da biyan bukatun bai daya na al’ummar duniya baki daya.

Xi ya kara da cewa, Sin a shirye take ta tabbatar da tsarin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, ya zamo mallakin al’ummun duniya baki daya, kuma za ta kare tsaro da daidaiton tsarin, kana za ta aiwatar da kwararan matakai na zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa, a fannin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, tare da tabbatar da cewa, dukkanin kasashen duniya sun ci gajiyar wannan ci gaba.  (Saminu Alhassan)