logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar zazzabin lassa ya karu zuwa 171 a Nijeriya

2022-09-19 10:38:49 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC), ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar kamuwa da zazzabin Lassa a kasar, ya karu zuwa 171, duk da matakan da gwamnati ta dauka na dakile yaduwarta.

A rahotonsa na baya bayan nan kan cutar ta Lassa, cibiyar NCDC ta ce tun daga farkon bana, an tabbatar mutane 917 sun kamu, yayin da ake zaton kamuwar wasu 6,660. Kuma daga makon 5 ga watan Satumba zuwa 11 ga watan kadai, an tabbatar da mutane 8 sun kamu, yayin mutum 1 ya mutu.

Kawo yanzu, jihohi 25 sun samu akalla mutum guda da ya kamu da cutar daga yankunan kananan hukumomi 102 daga cikin 774 dake fadin kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

A cewar cibiyar, adadin mace-macen ya kai kaso 18.6, wanda ya yi kasa da na makamancin lokacin a bara da ya dauki kaso 23.3 cikin dari.

Cibiyar ta ce rukunin wadanda cutar ta fi kamawa na tsakanin shekaru 21 zuwa 30, inda adadin maza da mata da aka tabbatar sun kamu yake kan 1:0.8. (Fa’iza Mustapha)