logo

HAUSA

Kasar Sin ta bada gudunmawar sama da kaso 30 ga ci gaban tattalin arzikin duniya daga 2013 zuwa 2021

2022-09-19 10:59:26 CMG Hausa

Matsakaicin gudunmawar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya zarce kaso 30 cikin dari tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021, inda ta kasance matsayi na daya a duniya.

Rahoton da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar, ya ce a cikin shekarar 2021 kadai, jimilar gudunmawar da Sin ta bayar ga tattalin arzikin duniya ya kai kaso 18.5 cikin dari, bayan musayar adadin bisa matsakaicin farashin musayar kudaden ketare, inda ta kasance matsayi na biyu a duniya. Haka kuma, adadin ya karu zuwa maki kaso 7.2 daga na shekarar 2012.

A cewar rahoton, tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021, matsakaicin karuwar alkaluman GDP na kasar Sin a kowace shekara, ya kai kaso 6.6, wanda ya dara kaso 2.6 na karuwar tattalin arzikin duniya da kuma kaso 3.7 na kasashe masu tasowa.

Haka kuma, kudin da kowane dan kasa ke samu ya kai CN Yuan 80,976, kwatankwain dala 11,684 a duk shekara, bayan cire haraji.

Bugu da kari, rahoton ya bayyana ci gaban da Sin ta samu daga kirkire kirekire a cikin shekaru 10 da suka gabata. A cewar kungiyar kula da hakkin mallakar fasaha ta duniya, kasar Sin ta kai mataki na 12 na ma’aunin kirkire-kirkire a duniya, daga mataki na 34 da ta kasance a shekarar 2012. (Fa’iza Mustapha)