logo

HAUSA

Aikin binciken duniyar Mars na kasar Sin ya samu kyawawan sakamakon kimiyya

2022-09-19 11:37:18 CMG Hausa

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, ta ce aikin binciken duniyar Mars da kasar ke yi ya samu kyawawan sakamako na kimiyya.

A cewar hukumar, zuwa ranar Alhamis, kumbon zagaye na Tianwen-1, ya yi aiki yadda ya kamata tsawon kwanaki 780, yayin da na’urar Zhurong mai tafiya, ta yi tafiya mita 1,921 a doron duniyar Mars.

Kumbon da na’urar na Tianwen-1, sun kammala ayyukan binciken kimiyya da ake son gudanarwa, inda suka tattaro bayanan kimiyya da suka kai yawan gigabyte 1,480.

Tianwen-1, ya kunshi kumbo da naurorin sauka da tafiya. A ranar 15 ga watan Mayun 2021, ya sauka a wurin da aka kebe na saukarsu a duniyar Mars, inda ya kasance kumbon bincike na kasar Sin na farko da ya sauka a duniyar Mars. (Fa’iza Mustapha)